Ya saukar da ruwa daga sama*, sai magudanai suka gudãna da gwargwadonsu, Sa'an nan kõgi ya ɗauki kumfa mai ƙãruwa, kuma daga abin da suke zuga a kansa (azurfa ko zinari kõ ƙarfe) a cikin wuta dõmin nẽman ado kõ kuwa kãyan ɗãki akwai kumfa misãlinsa (kumfar ruwa). Kamar wancan ne Allah Yake bayyana gaskiya da ƙarya. To, amma kumfa, sai ya tafi ƙẽƙasasshe, kumaamma abin da yake amfãnin mutãne sai ya zauna a cikin ƙasa. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana misãlai.
____________________
 * Idan ruwa ya sauka daga sama sa'an nan ya gudãna a cikin rãfuna zai yi kumfa. Sai ruwa mai amfãnin mutãne ya nutse a ƙasa ya zauna, sa'an nan kumfan kuma ya ƙeƙashe ya lãlãce. Haka kuma idan an sanya ƙarfe na zinãri kõ na azurfa kõ baƙin ƙarfe a cikin wuta, aka zuga ta a kansa, zai fitar da kumfa, wãtau tsakin tama wanda zã a fitar dõmin rashin amfãninsa, dõmin zĩnariyar ƙwarai mai amfãni ta wanzu. To haka ga kõme akwai kumfa marashin amfãni da mai kyãwo mai amfani.


الصفحة التالية
Icon