Kamar wancan ne Muka aika ka a cikin al'umma wanda take waɗansu al'ummai sun shũɗe daga gabaninta, dõmin ka karanta musu abin da Muka yi wahayi zuwa a gare ka, alhãli kuwa sũ, sunãkãfirta da Rahaman.* Ka ce: "Shi ne Ubangijĩna, bãbu abin, bautãwa fãce Shi, a gare Shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi tũbãta take."
____________________
   * Sũnan Allah Rahmãn, daga rahama, watau Mai Rahama wadda yake dukan alheri yanã shiga a cikin ma'anarta a wajen halitta da rãyuwa da bãyar da lãfiya da shiryarwa. Mafi girman nĩ'imarsa shĩ ne aikõwar Manzon Allah daga gare mu zuwa gare mu. Kãfirai ba su yi tunãni ba a kan waɗannan rahamõmi, balle su yi gõdiya, sabõda haka sai kãfirci suke yi.


الصفحة التالية
Icon