Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle ne, Muna jẽ wa ƙasar (su), Munã rage ta daga gẽfunanta? Kuma Allah ne Yake yin hukuncinsa. Babu mai bincike ga hukuncinsa. Kuma shĩ ne Mai gaggãwar sakamako.*
____________________
* Gaggãwar sakamako ga wanda ya ƙi bin umurnin Allah wanda Annabinsa ya iyar zuwa gare shi. Asalin hisãbi, shine bincike dõmin a sãmi abin da aka yi na alhħri kõ na sharri amma abin da ake nufi a nan maƙasũdin bincike shĩ ne sakamako da alhħri kõ da azãba, gwargwadon nufinSa.