Kuma waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Ba a aiko ka ba." Ka ce, "Allah Yã isa zama shaida a tsakãnina da tsakãninku da wanda yake a wurinsa akwai ilmin* Littãfi."
____________________
 * Allah Yã isa zama shaida, haka wanda yake a kan wani ilmi daga Allah kamar Yahudu da Nasãra sunã isa zama shaida a tsakãnĩna da ku a kan gaskiyar da'awã ta cewa nĩ abin aikõwa ne daga Allah zuwa gare ku dõmin akwai wannan magana a cikin littattafanku.


الصفحة التالية
Icon