Kuma Mun bai wa Mũsã* littafi, kuma Mun sanya shi shiriya ga Banĩ Isrã'ila, cẽwa kada ku riƙi wani wakĩli baiciNa.
____________________
* Tsakãnin Bãwan Allah Muhammadu da Mũsã, kuma an aiko Mũsã ga Banĩ Isrã'ila kawai, kuma Nũhu an ce masa bãwa amma ba a jingina shi kamar yadda aka jingina bawanSa ba. Sa'an nan kuma Jingina Yahũdu ga Nũhu ya daidaita su da sauran mutãne wajen da'awar ɗaukaka da nasaba.


الصفحة التالية
Icon