Kuma ka bai wa ma'abũcin zumunta hakkinsa* da miskĩna da ɗan hanya. Kuma kada ka bazzara dũkiyarka, bazzarãwa.
____________________
* Hakkin zumunta shi ne alheri da sãdar da zumunta. Hakkin miskini da ɗan hanya zakka da sadakar taɗawwa'i da liyãfar kwana uku ga bãƙo bisa al'ada da alheri, bã bisa ɓarna da kallafãwa ba.