Kuma idan ka karanta Alƙur'ani,* sai Mu sanya a tsakãninka da tsakanin waɗanda bã su yin ĩmãni da Lãhira wani shãmaki mai suturcẽwa.
____________________
* Mushirikai jahilai ne, ba su iya ɗaukar jãyayyar magana, sabõda sun fi kusanta zuwa ga dabbõbi ga tunãninsu, bisa gare su zuwa ga mutãne, kõ da yake sauran jikinsu na mutãne ne. Sabõda haka a kõ yaushe sunã kusa ga faɗan tãyar da hankali da dõke-dõke. Sabõda haka Allah Ya sanya tsari ga AnnabinSa da wanda ya bi hanyar Annabin, wajen shiryar da mutãne game da karanta Alƙur'ãni. Bã zã su iya fãɗa mai karanta Alƙur'ãni da dũka ba, kuma tsõronsa suke ji dõmin kwarjinin Alƙur'ãni.