Kuma ka cẽ wa bãyiNa, su faɗi kalma* wadda take mafi kyau. Lalle ne Shaiɗan yanã sanya ɓarna a tsakãninsu. Lalle ne Shaiɗan ya kasance ga mutum, maƙiyi bayyananne.
____________________
* Ka ce wa bãyĩNa, mutãne, idan sunã magana su auna kalmõmin da suke zance da su, sa'an nan su riƙa amfãni da kalma mafi kyãwo dõmin kada shaiɗan ya sãmi mashiga daga maganarsu zuwa ga zukãtansu, ya sanya ɓarna a tsakãninsu.