Ka ce: "Dã dai kũ, kunã mallakar* taskõkin rahamar Ubangijĩna, a lõkacin, haƙĩƙa dã kun kãme dõmin tsõron ƙãrẽwar taskõkin. Kuma mutum yã kasance mai ƙwauro ne."
____________________
* Muƙãrana a tsakãnin kyautar mutum da rõwarsa ga dũkiyar da ya mallaka.