Ka haƙurtar da ranka tãre da waɗanda ke kiran Ubangijinsu, sãfe da maraice, sunã nufin yardarSa. Kuma kada idãnunka su jũya daga barinsu, kanã nufin ƙawar rãyuwar dũniya.* Kuma kada ka biwanda Muka shagaltar da zũciyarsa daga hukuncinMu, kuma ya bi son zuciyarsa, alhãli kuwa al'amarinsa ya kasance yin ɓarna.
____________________
 * Ãyõyi na ashirin da bakwai da ashirin da takwas sunã umurni da bin shari'a ta Alƙur'ãni, kuma sunã hani daga bin son zũciya dõmin nħman ƙawar rãyuwar dũniya wadda aka yi dõmin a jarrabi wãwã da ita, sa'an nan ta kõma turɓãya ƙeƙasasshiya. Dũbi ãya kuma, ta takwas da ta tara. Mun dai sani, cewa umurni da bin sharĩ'a bayyananna shĩ ne kan labarin sũrar.


الصفحة التالية
Icon