Kuma waɗancan alƙaryu* Mun halaka su, a lõkacin da suka yi zãlunci, kuma Muka sanya lõkacin alkawarin, ga halaka(5) su.
____________________
* Alƙaryun Ãdãwa da samũdãwa da waɗansunsu. (5) Kõme Allah Zai yi, sai Yã sanya masa lõkacin aukuwarsa, kuma bã zai aukun ba sai ajalin nan da Ya ambata masa ya zo.