Sai suka sãmi wani bãwa daga bãyinMu, Mun bã shi wata rahama* daga wurinMu, kuma Mun sanar da shi wani ilmi daga gunMu.
____________________
  * Rahama a nan ita ce Annabci sabõda cħwa kuma an bã shi ilmi daga gun Allah, kuma ya yi hukunci da shi. Ilmin ilhãma bã a yin hukunci da shi dõmin Annabãwa kawai Allah Ya tsare daga kuskure game da wahayi. Wannan ne bambanci bayyananne a tsakanin wahayin Annabci da wahayin walicci. Haka mu'ijiza da karãma, su duka sãɓãwar al'ada ne, amma mu'ujizar Annabi an san zã ta zo daga bãkin wanda aka yi dõminsa, amma karãma bãbu mai saninta, sai tã auku. Sabõda waliyyi bã ya iya yin tãkara, amma annabi yana iya yin tãkara a kan maƙiyansa.


الصفحة التالية
Icon