Kuma idan waɗanda suka kãfirta suka gan ka, bã su riƙon ka fãce da izgili (sunã cẽwa), "Shin, wannan ne ke ambatar gumãkanku?" Alhãli kuwa sũ, ga ambatar Mai rahama, mãsu kãfirta* ne.
____________________
  * Sun kasance sunã aibanta wanda yake musun gumãkansu alhãli kuwa sũ, sunã musun zaman Allah Mai rahama ya kasance abin bautãwa guda. Wannan shi ne gãyar jãhilci.


الصفحة التالية
Icon