Kuma Muka sanar da shi sana'ar* wata tufa sabõda ku dõmin ya tsare ku daga makãminku. To, shin, ku mãsu gõdẽwa ne?
____________________
  * Wannan yanã nũna wajabcin yin sana'a wadda mutum ke rãyuwa a kanta. Kuma yanã nũna wajabcin aiki da sabubba dõmin neman tsaron kai. Bã ya halatta ga mutum ya yi kwance bãbu sanã'ar da zai tsayu a kanta Kõ kuma ya gĩtta kansa ga halaka da tãwilin tawakkali. Tawakkali shĩ ne mayar da ãƙibar al'amura ga Allah a bãyan mutum ya yi abinda yake iya yi.


الصفحة التالية
Icon