Sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka kuranye abin da ke a gare shi na cũta, kuma Muka kãwo masa mutãnesa da kwatank wacinsu tãre da su, sabõda rahama daga wurinMu da tunãtarwa* ga mãsu ibãda.
____________________
  * Ayyuba Manzon Allah, an jarrabe shi da wahalõlĩ ga jikinsa da halakar ɗiyansa ya yi haƙuri da hukuncin Allah, sai Allah Ya mayar masa da abin da ya halaka, sa'an nankuma ya ƙãrã masa wani kamarsa, dõmin rahamarSa ga mãsu mayar da al'amari a gare shi, da kuma wa'azi ga mãsuibãda dõmin kada aukuwar wata masĩfa ta sanya su kãtsewa da rashin ɗaukar haƙuri.


الصفحة التالية
Icon