Wanda ya kasance yanã zaton cẽwa Allah bã zai taimake shi* ba a cikin dũniya da Lãhira to sai ya mĩƙa wata igiya zuwa sama, sa'an nan kuma ya yanke ta, sa'an nan ya dũba. Shin, ko lalle kaidinsa zai gusar da abin da yake ji na takaici?
____________________
 * Wanda yake zaton Allah bã zai taimaki Annabinsa ba kuma yanã jin hushin Allah Ya zãɓi Muhammadu da Annabci, to, sai ya mutu da hushinsa,kuma ya yi dukan kaidin da yake so ya yi, Allah bã zai fãsa abin da Ya yi nufi ba a game da Annabinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.


الصفحة التالية
Icon