Waɗanda suke idan an ambaci Allah sai zukãtansu su firgita, da mãsu haƙuri a kan abin da ya sãme su, da mãsu tsayar da salla, kuma sunã ciyarwa daga abin da Muka azurta su.*
____________________
 * Waɗannan sũ ne siffõfin mãsu ƙasƙantar da kai watau mãsu tawãli'u. Zukãtansa na firgita idan an ambaci Allah, su ga kamar sunã ganin sa, a gaba gare su, sabõda haka sai su ji sauƙin haƙuri ga ɗaukar masifa, kuma su tsayar da salla da sauran ibãdõdi na jiki kuma su bãyar da zakka da sauran ibãdõdin dũkiya. 


الصفحة التالية
Icon