Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Waɗannan da hannuwanku na dãma suka mallaka da waɗanda ba su isa mafarki ba daga cikinku, su nẽmi izni* sau uku; daga gabãnin sallar alfijir da lõkacin da kuke ajiye tufãfinku sabõda zãfin rãnã, kuma daga bãyan sallar ishã'i. Sũ ne al'aurõri uku a gare ku. Bãbu laifi a kanku kuma bãbu a kansu a bãyansu. Sũ mãsu kẽwaya ne a kanku sãshenku a kan sãshe. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa a gare ku. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
____________________
* Ladabin shiga gida shĩ ne dukan yãron da ya balaga, ɗa ne kõ bãwa, kada ya shiga gida kõ a ɗãki a bãyan sallama sai ya nemi izni da cewa "In shiga?" Idan an karɓa masa da izni, ya shiga, idan kuma yanã zaton ba a ji shi ba, sai ya sãke neman izni har sau uku. neman izni yanã wajaba kõ ga yãran gidan a cikin lõkuta uku, wãtau a gabãnin sallar asuba da lõkacin tsakar rãnar na ƙailũla da bãyan sallar ishã'i.


الصفحة التالية
Icon