To, idan sun yi musu da kai, sai ka ce: "Nã sallama fuskata ga Allah, kuma wanda ya bi ni (haka)." Kuma ka ce wa waɗanda aka bai wa littãfi da Ummiyyai:* "Shin kun sallama?" To, idan sun sallama, haƙĩƙa, sun shiryu kuma idan sun jũya, to, kawai abinda ke kanka, shi ne iyarwa. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinSa.
____________________
* Ummiyyi shi ne wanda bai iya karatu da rubutu ba. A cikin Alƙur'ãni anã nufin Lãrabawa da wannan sunan, dõmin bã su da wani littãfin sama da suke da shi a lõkacin nan. Amma ba ana nufin bã su da rubutu ba. Haruffan rubutun Alƙur'ãni tun a zamãnin Ismã'ila ɗan Ibrãhĩma aka san su. Kuma a cikin Lãrabãwa da yawa sun san su, har sunã rubuta ƙasĩdu mãsu kyau, suna rãtayewa a cikin Ka'aba. Jahiliyya ita ce lõkacin da bã a aiki da wani littãfi na sama kamar yadda mafi yawan mutãne suke a yanzu, ƙarnin ishirin shi ma ƙarnin wata jahiliyya ne.


الصفحة التالية
Icon