To, a lõkacin da Mũsã ya yi nufin ya damƙi wanda yake maƙiyi ne a gare su, (mai nẽman ãgajin) ya ce,* "Ya Mũsã! Shin kanãnufin ka kashe ni ne kamar yadda ka kashe wani rai jiya? Ba ka son kõme fãce ka kasance mai tanƙwasawa** a cikin ƙasa kuma bã ka nufin ka kasance daga mãsu kyautatãwa."
____________________
* Ya faɗi haka zaton Mũsã zai kashe shi ne sabõda gargaɗin da ya gabãtar a gareshi, Maganar ta nũna Mũsã ya shahara da son gyãran abũbuwa dõmin islãhi, haka ne ga al'adar mutãne wanda ya tãshi yanã gyãra sai sun tuhumce shi da neman girma. ** Tanƙwasa ce sanya mutãne su yi abin da bã Su son yi. Kyautatãwar islãhi bã ta sãmuwa sai da tanƙwasãwa dõmin gãlibi mutãne sun fi son ɓarna a kan kyautatãwa tãre da saninsu ga cewar kyautatãwar ita ce daidai.