Kuma ba ya halatta ga mũmini kuma haka ga mũmina, a lõkacin da Allah da Manzonsa Ya hukunta wani umurni, wani zãɓi daga al'amarinsu ya kasance a gare su. Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, to, yã ɓace, ɓacẽwa bayyananna.*
____________________
* Wannan ãyã hani ne ga kõwane Musulmi kõ Musulma ga sãɓawa umurnin Allah da Manzonsa, su bi son rãyukansu ga kõme. Kuma ba a lõkacin auren Zainab da Zaidu ne ta sauka ba kamar yadda waɗansu mãsu tafsiri ke rubũtãwa dõmĩn an yi wannan aure a gabãnin hijira da nĩsa, ita ãyãr kuwa tã sauka a Madĩna ne a bãyan yãƙinAhzab, kamar yadda tsarin maganarta ya nũna.