Kuma ba su ƙaddara Allah a kan haƙĩƙanin* ĩkon yinsa ba: ¡asã duka damƙarSa ce, a Rãnar ¡iyãma, kuma sammai abũbuwan naɗewa ne ga dãmanSa. Tsarki ya tabbata a gare Shi, kuma Ya ɗaukaka daga barin abin da suke shirki da shi.
____________________
  * Yã yi bayãnin yadda zã a iya ƙaddara Allah a kan haƙĩƙanin ĩkon yinSa da cewa, "ƙasã duka damƙarSa ce har zuwa ƙarshen sũrar. Wãtau yã dunƙule sũrar abũbuwan da zã su auku a Rãnar Ƙiyãma dõmin su bai wa mai hankali yadda suranta ikon yi na Allah Mai girma zai yiwu.


الصفحة التالية
Icon