Kuma ba su rarraba ba fãce bãyan da ilmi ya jẽ musu, dõmin zãlunci a tsakãninsu kuma bã dõmin wata kalma* tã gabata ba daga Ubangijinka, zuwa ga wani ajali ambatacce, dã an yi hukunci a tsakaninsu. Kuma lalle ne waɗanda aka gãdar wa Littafi daga bãyansu, haƙiƙa, sunã cikin shakka a gare shi, mai sanya kokanto.
____________________
* Kalmar da ta gabãta, ita ce "Allah bã zai halaka mutane ba sabõda zunubi sai ajalinsu ya zo." Zãlunci da ke hana su haɗuwa a bãyan sanin gaskiya, shi ne hassadar jũna, sa kwaɗayi da son shugabanci a cikin mu'amala.