Kuma waɗanda suke kira baicinSa ba su mallaki cẽto ba, fãce wanda ya yi shaida da gaskiya, kuma sũ, sunã sane* (da haka).
____________________
 * Su waɗanda suka yi shaida da gaskiya sun san bãbu mai mallakar ceto ga wani fãce Allah. Sabõda haka Allah nã yi musu izni su ceci wanda Yake son su cece shi, ba wanda su suke so ba. Ma'anar iznin da ceto ga bãyin Allah sãlihai ita ce dõmin Allah Ya bayyana darajar mai ceton ne kawai, bã don yanã da wani hakki ba, ga Allah. Allah Ya tsarkaka daga wata halittarSa ta sãmi wani hakki a kanSa. Kõwa bãwanSa ne.


الصفحة التالية
Icon