Kuma Mun yi wasiyya ga mutum* game da mahaifansa biyu da kyautatãwa, uwarsa tã yi cikinsa wahala, kuma ta haife shi wahala. cikinsa da yãyensa watã talãtin. Har a lõkacin da ya kai ga mafi ƙarfinsa, kuma ya kai shẽkara arba'in, ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka kange nidõmin in gõde wa ni'imarKa, wadda Ka ni'imta a kaina da kuma a kan mahaifãna biyu, kuma dõmin in aikata aikin ƙwarai wanda Kake yarda da shi, kuma Ka kyautata mini a cikin zuriyata. Lalle nĩ, nã tũba zuwa gare Ka, kuma lalle ni, inã daga mãsu sallamãwa (ga umurninKa)."
____________________
* Mutum a cikin iyãlinsa, kõ ya zama mai gargaɗi ga kansa da nasĩha ga mahaifansa da zuriyarsa kamar yadda ya bayyana a cikin ãyõyi 13,l4 da l5, kõ kuma ya zama mai butulci ga kansa, ya tõzartar da iyãyensa da zuriyarsa, kamar yadda ya bayyanaa cikin ãyõyi 17 da 18.