Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Idan kun taimaki Allah, zai taimake ku, kuma Ya tabbatar da dugãduganku..*
____________________
* Tabbatar da dugadugan ƙafãfun, yanã nufin sanya musu jãrumta a cikin zukãtansu, dõmin ƙafãfunsu, su kafu a wurin yaƙi, dõmin kada su gudu.