Sabõda hakaa ka sani, cẽwa bãbu abin bautãwa fãce Allah, kuma ka nẽmi gãfara ga zunubin, ka,* (kuma sabõda mũminai maza da mũminai mãtã kuma Allah Ya san majũyaiku da mazauninku.
____________________
 * An umurci Annabi ya nemi gãfara dõmin mutãne su yi kõyi da shi, dõmin Allah Ya riga ya tsare shi daga zunubi a gabãni da bayan Manzanci.


الصفحة التالية
Icon