Lalle waɗanda ke yi maka mubãya'a,* Allah kawai ne suke yi wa mubãya'a, Hannun Allah nã bisa hannayensu, sabõda haka wanda ya warware, to, yanã warwarẽwa ne a kan kansa kawai, kuma wanda ya cika ga alkawarin da ya yi wa Allah a kansa, to, (Allah) zai kãwo masa ijãra mai girma.
____________________
* Asalin mubãya'a daga bai'u ne, watau ciniki, wanda ya yi mubãya'a ga Limãmin Musulmi kamar yã yi ciniki ne yã sayar da ransa, dõmin ya karɓi Aljanna daga Allah a Rãnar Ƙiyãma. Mubãya'a ta farko,ita ce wadda aka yi wa Annabi a Hudaibiyya wani ɗan gari ne kusa da Makka a hanyar Jidda, tafiyar kwana ɗaya. An ce tanã cikin Hurumi, waɗansu sun ce bã ta cikinsa.


الصفحة التالية
Icon