Kuma Allah Yã yi muku wa'adin waɗansu ganĩmõmi mãsu yawa, waɗanda zã ku karɓo su, kuma Ya gaggauta* muku wannan. Kuma Ya kange** hannãyen mutãne daga gare ku, kuma dõmin ta kasance wata ãyã ce ga mũminai, kuma Yã shiryar da ku ga hanya madaidaiciya.
____________________
* Cin nasara makusanci, shĩ ne cin Haibara, a bãyan kõmawar Annabi Madĩna a ƙarshen zul Hajji. Sa'an nan ya fita wajen ƙarshen Muharram shekara ta bakwai. Aka samo ganĩma mai yawa. Waɗansu ganĩmõmi na waɗansu ƙasãshen da zã a ci a nan gaba har ƙarshen dũniya. Ganĩmar Haibara ita ce aka gaggauta. ** A lõkacin da Annabi ya fita daga Madĩna zuwa Hudaibiyya Allah Ya kange hannuwan Yahũdãwa daga iyãlan Musulmi na cikin Madĩna, in dã bã dõmin haka ba sai su je su fãɗa su da kashi da kãmu. Sai Allah Ya jefa tsõro a cikin zukãtansu.