Muhammadu Manron Allah ne. Kuma waɗannan da ke tãre da shi mãsu tsanani ne a kan kãfirai, mãsu rahama ne a tsakãninsu, kanã ganin su sunã mãsu rukũ'i mãsu sujada, sunã nẽman falala* daga Ubangijinsu, da yardarSa. Alãmarsu tanã a cikin fuskõkinsu, daga kufan sujuda.** Wannan shĩ ne siffarsu a cikin Attaura. Kuma siffarsu, a cikin Injĩla ita ce kamar tsiron shũka wanda ya fitar da rẽshensa, sa'an nan ya ƙarfafa shi, ya yi kauri, sa'an nan ya daidaita a kan ƙafãfunsa, yanã bãyar da sha'awa ga mãsu shũkar' dõmin (Allah) Ya fusãtar da kãfirai game da su. Kuma Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga cikinsu, da gãfara da ijãra mai girma.
____________________
* Neman falala da sana'ar hannunsu, kõ fatauci, ba su zama nauyi a kan mutãne ba, kõwanensu ya dõgara ga Allah,sa'an nan yanã rãyuwa a kan hãlãliyarsa. ** Kufan sujuda, shĩ ne hasken fuskõkinsu da annurinsu. fuska ita ce madũbin zũciya. Anã gãne zũciyar ƙwarai daga fuskarta. Bã ya halatta ga mutum ya riƙa darkãka gõshinsa ga ƙasã dõmin ya yi kwãdon salla. Wannan alãmar riya ce. Faɗakarwa. Nan ne ƙarshen dõgãyen sũrõri da ake cewa Muɗawwalãtu. An ƙãresu da sũrõri biyu, Ƙitãl dõmin yãƙi, da fat'h dõmin tsãrin gudãnar da siyãsa sabõda tsaron Addĩni. Bãyan haka kuma sai gajerun sũrõri, watau Mufassalãtu.