Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan fãsiƙi* Yã zo muku da wani babban lãbãri, to, ku nẽmi bayãni, dõmin kada ku cũci waɗansu mutãne a cikin jãhilci, sabõda haka ku wãyi gari a kan abin da kuka aikata kunã mãsu nadãma.
____________________
* Idan wani yã kai lãbãrin ɓarna, kada a yi aiki da shi sai bãyan an bincika an san gaskiyar al'amarin, kãfin a yi aiki da shi. fãsiƙi ga asalin kalma shi ne duka wanda ya karkace daga hanyar ƙwarai wadda aka sani. A nan, fãsiƙi, shi ne mai kai lãbãrin da yake akwai tãshin hankali a cikinsa, ko kuma abin tsõro dõmin ya sanya rũɗu a tsakãnin jama'a tun ba a san haƙĩƙanin al'amarin ba.