Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnunMu, kuma ka tsarkake* Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye (dõmin salla kõ wani abu).
____________________
* (Ma'anar ita ce tsarkakewa kõ tasbĩhi, 'tsare sallõli, farillai, anã cewa' faɗin "Subhãnal lãhi wal Hamdu Lillãhi" a bãyan kõwane mazauni, dõmin ya zama kaffãrar wannan mazaunin.