Kuma idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba a cikin marãyu,* to, (akwai yadda zã a yi) ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba.
____________________
* Asalin marãya shĩ ne yãron da bai balaga ba, kuma ubansa ya mutu. Amma a cikin ãya-Allah Yã sani-anã nufin dukkan mai rauni a cikin al'umma, wanda yake neman a tsare haƙƙin sa da Allah Ya ɗõra wa Musulmi su tsare. Sabõda haka Ya shãfe jawãbin sharaɗin kuma Ya fãra da hukunce-hukunce, a kan tafsĩlin yadda zã a tsare mãsu rauni a cikin al'umma. Ya fãra da mãta a wajen aure, adadinsu daga ɗaya zuwa huɗu, gwargwadon ƙarfin mutum da iyãwarsa ga tsaida ãdalci a gare su, kõ a tsakãninsu. Ãdalci na kwãna da ciyarwa da tufãtarwa.


الصفحة التالية
Icon