Allah Yanã yi muku wasiyya a cikin 'ya'yanku; namiji yanã da rabon mãtã biyu. Idan sun kasance mãtã ne fiye da biyu kuwa, to, suna da biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari, kuma idan ta zama guda ce (kawai) to, tana da rabi. Kuma iyãyensa biyu kõwane ɗaya daga cikinsu yanã da ɗaya daga kashi shida ɗin abin da ya bari idan wani rẽshe ya kasance gare shi, to, idan rẽshe bai kasance gare shi ba, kuma iyãyensa ne (kawai) suka gãje shi, to, uwa tanã da sulusi (ɗaya daga cikin kashi uku). Sa'an nan idan 'yan'uwa sun kasance gare shi, to, uwarsa tana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida) daga bayan wasiyya wadda ya yi kõ kuwa bãshi. Ubanninku da 'yã'yan ku, ba ku sani ba, wannensu ne mafi kusantar amfani, a gare ku. Yankawa daga Allah. Lalle ne, Allah Yã kasance Masani Mai hikima.