Haƙĩƙa, lalle Mun aiko ManzanninMu da hujjõji bayyanannu, kuma Muka saukar da Littãfi da sikẽli tãre da su dõmin mutãne su tsayu da ãdalci, kuma Mun saukar da baƙin ƙarfe,* a cikinsa akwai cutarwa mai tsanani da amfãni ga mutãne, kuma dõmin Allah Ya san mai taimakonSa da ManzanninSa a fake. Lalle ne Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi.
____________________
 * Littafi a nan anã nufin dukkan Littattafan samã da aka bãyar a bãyan Nũhu da Ibrahĩm. Ma'auni kuma, shi ne sharĩ'ar da ke cikinsu. Baƙin ƙarfe kuwa dõmin kãyan aiki na amfãnin sana'õ'i da cũtar da ke a cikinsa na makãmai da kuma amfãnin tsaron addini da jihãdi. Littafi da ma'auni ana aiki da su wajen awon ibãdar Allah da mu'ãmalõli a tsakãnin mutãne.


الصفحة التالية
Icon