Dõmin kada (5)mutãnen Littãfi su san cẽwa lalle bã su da ikon yi ga kõme na falalar Allah, kuma ita falalar ga hannun Allah kawai take, Yanã bãyar da ita ga wanda Ya so (wannan jãhilci yã hana su ĩmani). Kuma Alah Mai falala ne mai girma.
____________________
  (5) Rashin saninsu ya hana su su bi Mahammadu ga sãmun falalar Allah; rabo biyu. Ga wata fassara, an ce harafin korewa ƙãri ne, watau ma'anarsa ita ce Allah Yã bãyar da rabo biyu ga waɗanda suka yi ĩmãni da Mazonsa, dõmin mutãnen littafi su san ba zã su iya hana abin da Allah Ya nufa ba.


الصفحة التالية
Icon