Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan an ce muka, *"Ku yalwatã a cikin majalisai," to, ku yalwatã, sai Allah Ya yalwatã muku, kuma idan an ce muku, "Ku tãshi" to, ku tãshi. Allah nã ɗaukaka waɗanda suka yi ĩmãni daga cikinku da waɗanda aka bai wa ilim wasu darajõji mãsu yawa, kuma, Allah Mai ƙididdigewa ne ga dukan kõme.
____________________
  * Bãyan ƙissar hukuncin gãnãwa cikin majalisa, sai kuma hukuncin zaunãwa kõ tãshi dõmin wani ya zauna. Kuma ana fifita mãsu ilmi da zama ga wurin da ya fi dãcewa da su.


الصفحة التالية
Icon