Shĩ ne wanda Ya aika, a cikin mabiya al'ãdu,* wani Manzo daga gare su yanã karanta ãyõyinSa a kansu, kuma yanã tsarkake su, kuma yanã sanar da su littafin da hikimarsa kõ da yake sun kasance daga gabãninsa lalle sunã a cikin ɓata bayyanãnna.
____________________
  * Lãrabawa sũ ne mabiya al'ãdu, watau ummiyyũn daga ummu, watau uwa watau kamar yadda uwãye suka haife su dõmin bã su da wani littãfi da suke bi sai al'ãdunsu da hukunce-hukuncen shaihunansu.


الصفحة التالية
Icon