Kuma wanda* bai sãmi wadãta ba daga cikinku bisa ga ya auri 'ya'ya mũminai, to, (ya aura) daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, daga kuyanginku mũminai. Kuma Allah ne Mafi sani ga ĩmãninku, sãshenku daga** sãshe. Sai ku aurẽ su da izinin mutãnensu. Kuma ku bã su ijãrõrinsu bisa ga abin da aka sani, suna mãsu kamun kai bã mãsu zina ba, kuma bã mãsu riƙon abõkai ba. To, idan aka aure su, sai kuma suka zo da wata alfãsha, to, akwai a kansu rabin abin da ko a kan, 'ya'ya daga azãba. wancan (auren kuyanga) ga wanda ya ji tsõron wahala ne daga gare ku. Kuma ku yi haƙuri shi ne mafi alhẽri a gare ku. Kuma Allah Mai gãfara ne Mai jin ƙai.
____________________
* Hukunce-hukuncen auren kuyanga ga wanda bai sãmi ĩkon auren'ya ba. Aibin auren kuyangi shi ne bautar da zuriya, domin bauta daga uwa take. Saboda haka bã ya halatta ga Musulmi ya auri baiwar kafiri, kome larurar da take ciki,sai dai ya saye ta daga gare shi.. **Ku duka daidai kukewajen ĩmãni da Musulunci. Dubi kuma Ãli'Imrãna 195.


الصفحة التالية
Icon