Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan anyi kirã zuwã ga salla a rãnar Jumu'a, sai ku yi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar* ciniki. Wancan ɗinku ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani.
____________________
* Ba a hana Musulmi aiki ba a kõwace rãna, sai dai an hana duk wanda Jumu'a ta lazimta a kansa da ya yi wani aiki wanda bã na tattalin salla ba a rãnar Jumma'a, a bãyan kiran salla. Anã nufi da kiran salla na biyu a bãyan limãmi ya zauna a kan mumbarinsa, dõmin wannan kiran aka sani azãmanin Annabi da Abubakar da Umar. Amma kira na farko, Usman bn Affãn ne ya fãra shi dõmin farkar da mutãne, a bãyan sun yi yawa kuma sun kama sana'õ'i. Kuma a bãyan an ƙãre salla, sai a wãtse zuwa ga ayyuka da neman abinci. Bã a tsayãwa yin wata nãfila a bãyan sallar Jumu'a, sai dai an so yin raka'a biyu a bãyan fita daga masallãci kamar yadda Annabi ke yi. A farko, anã yin huɗubar sallar Jumma'a a bãyan salla har a lõkacin da ãyarin Dihyatul Kalbi ya kõmo daga shãm (Syria) da abinci,ya sauka a Baƙĩ'a, suka buga ganga, sai Sahabbai suka fita dõmin neman sayen abincin a gabãnin a ƙãre huɗubar suka bar mutum gõma shã biyu tãre da Annabi. Sai aka mayar da huɗubar a gabãnin salla. Kuma an fahimci cewa anã yin huɗuba a tsaye. Kuma ba a kafa Jumu'a, sai a kafaffen gari, amma Jumu'a nã ƙulluwa da mutum gõma sha biyu da lĩman.


الصفحة التالية
Icon