"Fãce ga wanda Yã yarda da shi, wato wani manzo sa'an nan lalle ne, zai sanya* gãdi a gaba gare shi da bãya gare shi."
____________________
* ldan Allah Yã aiko wani manzonsa da wani umurni ko hani zuwa ga mutãne to zai sanya mala'iku gaba gare shi da bãya gare shi suna gãdin sa dõmin kada wani Shaiɗãni ya kusance shi har ya sanya shi mantuwa ko kuskure, har ya iyar da manzancin nan kamar yadda yake.