Yã kũ waɗanda suka yiĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga ManzonSa, da ma'abũta al'amari daga cikinku.* Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. wannan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara.
____________________
* Haka su kuma mutãne talakãwa, amãna ce a kansu su yarda da hukuncin Allah da Manzonsa, a kome na al'amurransu da mu'ãmalõlinsu. Kuma wãjibi ne a kansu su yarda da abin da aka hukunta a kansu daidai da sharĩ'ar Allah. Su kuma idan sun sãɓa, to, sun yaudari amãnar Allah ke nan.