Kuma Allah ke da* (mallakar) abin da ke cikin sammai da kuma abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yã kasance, a dukkan, kõme, Mai kẽwayewa.
____________________
* Ko da yake Allah Yã riƙi Ibrãhĩma "Khalĩl" watau masõyi, amma bai hana Ibrahĩma ya zama a cikin bãyin Allah kuma mulkinSa ba, domin yana daga cikin abin da sama da ƙasa suka ƙunsa a cikinsu.