"Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa."*
____________________
* Shaiɗan yakan ɓõye idan ya ji an ambaci sunan Allah, dõmin haka aka yi masa suna mai ɓõyewa, wãto bã ya zuwa wurin da ake karatu da wa'azi, kamar yadda bã ya zama cikin zũciyar mutum mai ibãda da gaskiya. Ibãda ta gaskiya ita ce wadda aka yi ta kamar yadda Allah Ya ce a yi ta. Banda ibãdar bidi'a, ba ta korar Shaiɗan. Kuma da sharaɗin a yi ibãdar da kyakkyawar niyya, dõmin aikin da bãbu niyya mai kyãwu game da shi ɓãtacce ne.