Allah bã Ya son bayyanãwa da mũnãna daga magana* fãce ga wanda aka zãlunta. Kuma Allah Yã kasance Mai ji, Masani.
____________________
* Magana mummũna. Allah bã Ya son bayyana mugunyar magana, sai dai wanda aka zãlunta, yana iya kai ƙãra, kuma yana iya yin addu'a a kan wanda ya zãlunce shi. Sa'an nan ya shiga bayyanãwar abin da ake nufi da miyagun maganganu a cikin ãyõyin da suke bin wannan.