Kuma lalle Allah Yã riƙi alkawarin Banĩ lsrã' ĩla kuma Muka ayyana wakilai gõma shã biyu* daga gare su kuma Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ, Inã tãre da ku, haƙĩƙa, idan kun tsayar da salla, kuma kun bãyar da zakka, kuma kun yi ĩmani da manzannĩNa, kuma kuka taimake su, kuma kuka bai wa Allah rance mai kyau, haƙĩƙa, Inã kankare laifukanku daga gare ku, kuma haƙĩƙa, Inã shigar da ku gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sanã gudãna a ƙarƙashinsu, sa'an nan wanda ya kãfirta a bãyan wannan daga gare ku, to, lalle ne, yã ɓace daga tsakar hanya."
____________________
* An ayyana wakilai goma shabiyu daga ƙabĩlun Bani Isrãĩla goma sha biyu domin su ɗaukar musu alkawari daga wurin, kuma su tsare mutãnensu ga ganin ba a sãɓa wa alkawarin ba. An gina addinin Bani Isrãĩla a kan ƙabĩlanci. Saboda haka addininsu bã ya fita daga dã'irarsu.