Wasu maza biyu* daga waɗanda suke tsõron Allah, Allah Yã yi ni'ima a kansu, suka ce: "Ku shiga gare su, daga ƙõfar, dõmin idan kuka shige shi, to, lalle ne ku, mãsu rinjãya ne, kuma ga Allah sai ku dogara idan kun kasance muminai."
____________________
* Maza biyu su ne Yusha'u da Kãlib daga Nuƙabã'u, watau wakilai goma sha biyu waɗanda Annabi Musã ya aike su domin su yiwo binciken hãlãyen mutanen da suke zaune a cikin Ƙudus. Yadda ya fãru shi ne, bãyan da Allah Ya halaka Fir'auna sai Bani Isrã'ĩla suka koma Masar, daga nan sai Allah Ya rubuta musu cewa su tashi su koma Ariha'a, a cikin ƙasar Sham alhãli mazaunanta kuwa Kan'aniyyawa ne. Sai Musã ya gaya musu cewa, ga ƙasar da Allah Ya bã su, su fitar da waɗanda ke a ciki su zauna. Musã ya aika da mutum goma sha biyu domin su yiwo leƙen asiri su zo masa da lãbãri, kada su gaya wa mutãne abin da suka gani domin kada su firgita. Bayan da suka kõmo, sai suka warware alkawarin; sai mutum biyu daga cikin su, Yusha'u da Kãlib.


الصفحة التالية
Icon