Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku nemi tsari zuwa gare shi, kuma ku yi jihãdi* a cikin hanyarsa, tsammãninku, za ku ci nasara.
____________________
 * Wasĩla ita ce dukkan aikin ibãda wanda zai kusantar da mutum zuwa ga Ubangijinsa, amma da sharaɗin an gina shi a kan taƙawa. Kuma taƙawa ita ce bin Allah kamar yadda Ya yi umurni a bi Shi, ta hanyar manzonSa kawai. Jihãdi yana cikin taƙawa amma Yã kõma ambatonsa ne domin muhimmancinsa. Shi kuma iri biyu ne: ƙararmi, watau yãƙin abokan gãbã na bayyane, da babba, shi ne yãƙin abokan gãbã na ɓoye, watau rai da shaiɗan. Wanda maƙiyinsa na bayyane ya kashe shi yã mutu shahĩdi, wanda maƙiyinsa na ɓoye ya kashe shĩ ya mutu fãsiƙi ko kãfiri watau shaƙiyyi.


الصفحة التالية
Icon