Ka ce: "Ashe kunã bauta wa, baicin Allah, abin da ba ya mallakar wata cuta sabõda ku kuma haka wani amfani* alhãli kuwa Allah Shi ne Mai ji, Masani?"
____________________
* Idan bauta wa Ĩsã, Annabin Allah ya zama kãfirci bauta wa waliy yã zama shirka kenen. Kuma idan Ĩsã bai mallaki kõme ba, to, waliyyi mene ne matsayinsa?.