Lalle ne kana sãmun mafiya tsananin mutãne a adãwa ga waɗanda suka yi ĩmãni, Yahudu ne da waɗanda suka yi shirki. Kuma lalle ne kanã sãmun mafiya kusantarsu a sõyayya ga waɗanda suka yi ĩmãni su ne waɗanda suka ce: "Lalle mu ne Nasãra." Wancan kuwa sabõda akwai ¡issawa da ruhubãnãwa* daga cikinsu. Kuma lalle ne su, bã su yin girman kai.
____________________
  * Ƙissĩsi shĩ ne lĩmãnin kiristãwa, ruhubãnanci shĩ ne mutum ya tsabbace daga mutãne dõmin ibãda, kuma ba ya yin aure. Baruhubãne guda, ruhubãnãwa jam'i.


الصفحة التالية
Icon